Amazon zai bude shagon sayar da litattafai

Image caption Shagon sayar da litattafai

Katafaren kamfanin sayar da kayayyaki ta hanyar intanet Amazon zai bude shagon gama-gari na sayar da litattafai a Seattle, a wani yunkuri na fadada hada-hadar kasuwancinsa.

Kamfanin na Amazon zai rika sayar da akasarin litattafan da ya ke sayarwa a Amazon.com, kuma farashinsu zai zama daya da wadanda ya ke sayarwa a shafinsa na intanet.

Kazalika, mutane za su iya sayan wasu na'urorin da kamfanin ya ke sayarwa ta intanet a sabon shagon da zai bude, kamar na'urar karatu ta Kindle da kuma Fire TV.

Mataimakiyar shugaban sashin sayar da litattafai na Amazon, Jennifer Cast ce ta sanar da shirin Amazon na bude sabon shagon na sa mai kofofin katako.

Za a sanya kimanin litattafai dubu 5 a shagon, kuma akasarinsu wadanda mutane suka fi nuna sha'warsu a kansu ne, da wadanda mutane suka ce a kawo musu, da kuma wadanda a ka ga mutane sun fi son su karanta.

Sai daiw asu kamfanonin da ke gogayya da Amazon sun soki shirin bude shagon, inda suka ce ya sabama tsarinsa na rashin kasa litattafai a kan kanta.

Daya daga cikin masu gogayya da Amazon, Waterstones ya ce zai dai na sayar da na'urar karatu ta Amazon, Kindle a shagungunansa.