Yadda kyankyasai za su iya ceton rayuwa

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

An san kyankyasai na da alaka da dauda da maikwo da a kan samu a kicin da kuma ban-daki, inda da zarar an shigo daki an kuna wuta, za ka ga suna neman mafaka.

Wata marubuciya Mary Colwell ta ce, yanzu ba masu maganin kwari kadai ne ke neman su ba, har da masu bincike a kan kwayoyi da butum-butumi da kuma masu hada sassan jiki na roba ma na neman kyankyasai.

A Havana, kyankyasun garin na da koriyar kala, kuma yawanci su na masa ajiyar kulawa ne, inda har ake tatsuniya da shi.

Akwai wata tatsuniyar da ta bayar da labarin wata 'yar kyakkyawar kyankyaso mai suna Martina, wacce ta ke gwada hankulan maneman ta.

Kakarta ta bata shawarar cewa "Ki zuba ruwan shayi a takalman su, ki ga abin da za su yi, saboda ya kamata ki san halin mijin da za ki aura, har dai lokacin da yake fushi".

Dukkansu sun nuna halinsu, da ta yi masu gwajin shayin, amma wani talaka salihi mai hankali daga ciki ne ya yi nasara, kuma shi ta aura.

Wadannan kwari dai ba sa samun shaida mai kyau duk da cewar, ba su cancanci karar tsanan da aka dora masu ba.

Cikin kalan kyankyasai 4,500 da aka sani a duniya, hudu daga cikin su kadai ake yi wa ajiyar kulawa, kuma yawanci ba sa zama tsakanin mutane, duk da cewar suna bayar da muhimmiyar gudunmuwa ga muhalli, ta hanyar cin abubuwan da suka rube.

Akwai wasu kyankyasai masu zane da kaloli na ban sha'awa, wasu suna da ilimin zumunci, inda suke sada sakonni ga juna game da inda akwai abinci ko wurin zama, wasu kuma suna zaman kadaici, yayin da wasu kuma suke zaune tare suna kulawa da 'yan uwansu.

Image caption Wannan wasu kalan kyankyason da ake cewa 'Dwarf hissers' ne kan wani dutse a gidan ajiyar dabbobi na Tsimanampetsotsa National Park da ke kasar Madagascar.

Kyankyasai kan yi kara daban-daban domin jan hankulan juna ga jima'i, suna kuma da juriya, inda wasu ke iya yin watanni da abinci kalilan, misali wani irin kyankyaso da ake cewa 'Eublaberus Posticus', zai iya shekara yana shan ruwa kadai.

A watan Yuni ne, wasu dalibai a jami'ar Shanghai Jiao Tong suka gano yadda za su iya sanya wa kyankyasai tunanin su, inda suka sanya masu wata na'urar da ta cusa wa kyankyasan ra'ayin gina tururuwa.

Image caption Wani kyankyaso da aka yi wa mai 'bincike da ceto rayuwa' wanda aka kirkiro da shi ajami'ar North Carolina.

Akwai bincike kan kyankyasai da aka gudanar da ke da alaka da kwayoyi, inda masana kimiyya suka binciki yadda kyankyasai ke iya zama cikin dauda ba tare da ta masu wata illa ba, kuma suka gano cewar suna da kwayoyin halittu a jikinsu da ke masu magani.

Dalilin haka ne ake tunanin kyankyasai na da kwayoyin halittu a jikin su da za su taimaka wurin samun magungunan cututtukan da ke da alaka da kwayoyin cuta, watau E.Coli da MRSA, da ma wasu cututtukan da ke da wahala wurin warkewa.

Ana cin kwari a kasar China, inda wasu suka fi son cin wani irin kyankyaso da ake cewa 'American Cockroach' bayan an soye su.