Koyar da karatu da wayar salula a Kenya

Hakkin mallakar hoto Toni Maraviglia
Image caption Toni Maraviglia da abokin aikinta Kago Kagichiri

Toni Maraviglia daya daga cikin wadanda suka samar da wata manhaja ta yin karatu da wayar salula a Kenya ta ce "Na tuna da irin wahalar da malamai suka sha a lokacin da nake zaune a wannan kauyen."

Daga abin da ta sani na rayuwa, Ms Maraviglia 'yar kasar Amurka mai kimanin shekaru 32 a duniya wadda ta je kasar Kenya domin ta koyar, ta yi tunanin kirkiro da wata hanya ta koyarwa da wayar salula ta hanyar tura sakonnin kar ta kwana.

Tare da hadin gwiwar Kago Kagichiri sun kafa harkokin kasuwancin su a Nairobi a shekarar 2011.

Eneza ta ce tana son a mayar da dalibai miliyan 50 kwararru wajen neman ilimi ta hanyar salula da sauran kafafan sadarwa.

Mutane da dama na ganin cewa kamfaninmu baya samun wata riba, saboda ni macece kuma ak an harkar ilimi aka kafa kamfanin. Eneza ta ce "Mu muna da manufa, abin da muke caji bai taka kara ya karya ba."

Hakkin mallakar hoto Toni Maraviglia
Image caption Toni Maraviglia a wajen koyarwa a kauyen Kenya

Ga matasan da ke sauran sassan nahiyar Afrika, ilimi ya zamo ruwan dare a gare su, da ma iyalansu.

A makarantun gwamnati da suke da saukin kudi, azuzuwa na cike makil, malaman a gajiye ga karancin litattafan karatu da ake cewa textbooks, yayin da a makarantu masu zaman kansu su kuma akwai tsada.

Ms Maraviglia wadda ta fara koyarwa a birnin New York, ta tsani bangaren fasahar sadarwa, shi kuwa abokin aikinta Mr Kagichiri malami ne wanda ya tsani koyarwa kuma.

Hakkin mallakar hoto Toni Maraviglia
Image caption Dalibai na koyon karatu da wayar salula

Daliban Eneza sun kai dubu 500, kuma suna yin darrusa da muhawara ta hanyar sakonnin karta kwana a kan kudi kalilan wanda ake zara a duk mako.

Amfanin da ake yi wajen tura sakonnin karta kwana ya bawa masu amfani da wayoyin salula a kauyukan Kenya damar ci gaba da karatun su ko da kuwa akwai matsalar 'network'.

Kamfanin Eneza ya fi mayar da hankali wajen koyar da yara daga shekara 10-18 karatu, amma kuma yana koyar da wadanda aka kore su daga makaranta ma wadanda ba su wuce shekara 25 ba.

Kazalika kamfanin ya na koyar da darussa irin na kasar Kenya da suka hadar da lissafi da kimiyya da Kiswahili da kuma Ingilishi.

Wata mata Beatrice Wambui ta kasance tana yawan amfani da shafin kamfanin Eneza ta ce da shili 10 kawai ana bawa yaronta ilimi a kowacce rana.