An gargadi masu zabe a Myanmar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An gargadi mutane kan Aung Suu Kyi

Shugaban kasar Myanmar Thein Sein ya gargadi mutanen kasar da kada su kadawa 'yar takarar jami'iyyar adawa ta Aung Suu Kyi kuri'unsu.

A wani jawabi da ya yi wa al'umar kasar ta gidan rediyo kwanaki shida kafin zaben, Mr Thein ya ce idan aka matsa da aiwatar da sauye sauye cikin gagawa, hakan ka iya haifar da yakin basasa da bore irin wadanda kasashen larabawa suka fuskanta.

Ana sa ran jam'iyyar Aung San Suu Kyi za ta ci yawancin kujeru, sai dai tsarin mulkin kasar ya haramta wa mata zama shugabar kasar.

Da dama na ganin cewar Aung San Suu Kyi ba za ta iya kulla dangantakar aiki ba tare da sojojin Myanmar.