An kai samame kan ofishin hukumar kwallon kafar Jamus

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Ana zargin wasu jami'an FIFA da hannu a wajen kin biyan haraji.

'Yan sandan Jamus sun kai samame kan hedikwatar hukumar kwallon kafar kasar, DFB a kan zargin kauce wa biyan haraji dangane da bayar da izinin daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta shekarar 2006.

Wata sanarwa da masu shigar da kara suka fitar ta ce suna yin bincike kan kudi $7m da hukumar ta aike da su ga hukumar FIFA.

Da ma dai ana zargin cewa an ajiye kudin ne domin Jamus ta samu damar sayen kuri'u da za su taimaka mata samun damar daukar nauyin gudanar da gasar, ko da ya ke ta musanta zargin.

Kafafen watsa labaran Jamus sun ce an kai samame a kan gidan shugaban hukumar Wolfgang Niersbach da wanda ya gabace shi Theo Zwanziger.