Kotu ta ce a bai wa Dasuki fasfo dinsa

Image caption Sambo Dasuki a lokacin zaman kotu a watan Satumba

Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ta ba da umarnin a gaggauta bai wa tsohon mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro, Kanar Sambo Dasuki ritaya, fasfo dinsa, domin ya samu damar zuwa kasar waje domin a duba lafiyarsa.

Sambo Dasuki dai na fuskantar tuhuma ne kan zargin mallakar makamai a gidansa, da kuma na halatta kudaden haram.

A bisa wannan dalili ne aka kwace fasfo din na sa a kan sharadin bayar da belinsa.

Alkalin kotun, mai shari'a Ademola Adeniyi ya ce a gwamnati ta saki fasfo din Kanar Sambo domin ya sami damar zuwa asibiti a kasar waje a duba lafiyar sa.

Likitan da ke duba Sambo Dasuki a Biritaniya ne ya aiko da wasika cewa lallai ya kamata wanda ake tuhuma din ya je can don a duba lafiyarsa, a daya hannun kuma bangaren gwamnati sun gabatar da tasu hujjar inda suka gabatar da wasika daga shugaban asibitin kasa watau National Hospital wanda ya rubuto cewa ko a Najeriya ana iya duba mai fama da cutar daji wato cancer.

Kotun a shari'ar da ta yanke, ta bukaci Sambo Dasuki ya gabatar da wani mutum da zai tsaya masa, kuma idan har wa'adin da kotu ta dibar masa na makonni uku ya cika ba tare da ya dawo ba, to kotun za ta kama wannan mutumi a madadin Dasuki.

Sharadi na biyu kuma shi ne ana so ya dawo da fasfo dinsa ga hukumar tsaro ta farin kaya cikin sa'o'i 72 da dawowarsa.

Za a ci gaba da zaman kotu da sauraran wannan kara ta Sambo Dasuki a ranar 26 ga watan Nuwamba mai zuwa.