Ministoci: Saraki ya gana da Buhari

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Saraki na fuskantar shari'a kan batun kaddararsa

Shugaban majalisar dattawan Nigeria, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya mika wa Shugaba Muhammadu Buhari sunayen mutane 36 da majalisar ta tantance su a matsayin ministocin kasar.

Sanata Saraki ya isa fadar Aso Rock ne a Abuja inda ya mika takardar sunayen ministocin tare da masu bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisa; Sanata Ita Enang da Abdurahman Kawu Sumaila.

A jawabinsa, Sanata Saraki ya ce majalisar ta amince da dukka mutane 36 da shugaban kasar ya aike mata domin nada su a matsayin ministoci.

Daga bisani shugabannin biyu sun yi tattaunawar sirri a cikin ofishin shugaban kasa inda sauran manyan jami'an gwamnati suka fita suka bar su.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate

A ranar 29 ga watan Oktoba, majalisar dattawan ta kammala tantance ministoci 36 da shugaba Buhari ya aika mata.