"Bom ne ya sa jirgin Rasha ya fadi"

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sakataren harkokin wajen Burtaniya Philip Hammond

Burtaniya ta ce akwai yiwuwar jirgin saman kasar Rasha da ya yi hadari a Masar ranar Asabar, ya fadi ne sakamakon fashewar bom.

Sakataren harkokin wajen kasar, Philip Hammond, ya ce sun fahimci haka ne bayan sun yi nazari kan wasu bayanan sirri da suka tattara daga majiyoyi da dama.

Jami'ai a Amurka ma sun ce bom ne ya yi sanadiyar faduwar jirgin, sai dai sun ce wannan ba shi ne sakamakon karshe na bincikensu ba.

Wani jami'in Amurka ya ce mai yiwuwa mayakan kungiyar IS, wadanda suka yi ikirarin kakkabo jirgin daga farko, su ne ke da alhakin harbo shi.

Burtaniya ta dakatar da jiragen kasar zuwa birnin Sharm el-Sheik na Masar da ake zuwa yawon bude ido, inda daga nan ne jirgin Rashan da ya fadi ya taso.

Kwararru a fannin sufurin jiragen sama a Burtaniya za su je kasar Masar domin yin nazarin al'amuran da suka shafi tsaro a harkar sufurin jiragen sama.

Mutane 224 da ke cikin jirgin kasar Rashan ne suka mutu lokacin da jirgin ya fado a kan hanyar sa ta zuwa birnin St Petersburg na Rasha.