Abubuwa biyar da ke gaban shugaba Buhari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya ke zagaye dandalin Eagle Square na Abuja, domin duba jerin sojoji da suka yi fareti a ranar rantsarwar sa.

An rantsar da shugaba Buhari, a ranar 29 ga watan Mayun bana, kuma mutum ne da ya bambamta da sauran 'yan siyasa da aka saba gani, domin halayyarsa ta kyamar karbar hanci, da kwar jini da kuma sanin ya kamata.

Ya kama da lakanin da aka yi masa na "Baba Go-Slow", watau 'Baba mai tafiyar hawainiya'.

Duk da haka, rashin hanzarin Buhari na da tasa matsalar, tun da sai da ya dauki tsawon watanni hudu kafin ya nada majalisar zartarwarsa, wadda ba wasu mutane ne da ba a sani ba.

Yanzu haka akwai kalubale dayawa da Najeriya, wacce ta fi kowace kasa yawan al'umma a Afrika za ta fuskanta game da ci gaban tattalin arziki.

Farashin mai ya sauka, darajar kudi ta fadi sannan kuma kungiyar Boko Haram ta addabi yankin, inda daga watan Yuni zuwa yanzu suka kashe mutane sama da 1,700.

Al'ummar Najeriya na fatan sabbin manufofin da shugaban na su ya zo da su, za su kawo sauyin da suke bukata nan ba da dadewa ba.

Jaridar Washington Post ta Amurka ta yi nazari a kan wasu abubuwa biyar da ta ce Buhari zai iya yi domin kawo sauyi a kasar

1 A yi sharar cikin gida: Tsarin da Buhari ya fitar zai fuskanci kalubale a wurin tsofaffin 'yan siyasa a jam'iyyarsa ta APC, wadanda ake zargi da hannu dumu-dumu a karbar hanci.

Ya kamata Buhari ya kori duk wasu da ake zargi da hannu a karbar hanci, wadanda za su iya bata masa 'wasa' kamar yadda Carl LeVan ya bayyana a littafin sa na kwanan nan.

An dai san da cewar sharar cikin gida za ta iya janyo wa Buhari matsala a siyasarsa, tun da an sani cewar yawancin masu goyon bayansa sun tsallako ne daga jami'yyar abokin takararsa, Goodluck Jonathan na PDP.

Dalilin haka akwai yiwuwar in har ya takura masu, za su iya koma wa ga jam'iyyar su ta asali su hade masa kai.

2 A rage ma'aikatun gwamnati: Buhari ya na da damar rage kudin da gwamnati ke kashewa in har ya soke wasu daga cikin ma'aikatu 500 da kasar ke da su.

Wasu masana suna zargin cewa ana bude wasu ma'aikatun ne saboda a samu hadin kai da kara zumunci tsakanin 'yan siyasa.

Wadannan ma'aikatun da wasu ke da amfani kuma wasu babu dalilinsu, a nan ne dandalin karbar hanci da rashawa suka fi katutu, wani bayani mai sarkakkiya da Daniel Jordan Smith ya fayyace.

Buhari ma zai iya soke wasu ma'aikatun da ke da kyau amma amfaninsu bai da wani muhimmanci, misali menene dalilin kashe sama da dala miliyan hudu a kan Cibiyar tashar hawa sama jannati, watau 'Center for Space Transport and Propulsion'?

3 Yanka babbar giwa: Wasa wuka da Buhari ya yi na kawo sauyi ga manyan ma'aikatu biyu na kasar, wadanda suka hada da ma'aikatar man fetur da ta sarrafa karafuna, ya sa masana cikin damuwa.

An jima ana kashewa irin wuraren nan makuden kudade da ba a gani a kasa ba, sai dai ma kasar ta samu faduwa.

An samu shugabanni shekaru da dama da suka zuba kudi a ma'aikatun nan, saboda kamar yadda Robinson da Torvik suka bayyana, ayyukan ba sa riba.

Buhari dai yana iya shiga rudani kamar sauran jama'a, inda manufufinsa na rubanya riba daga albarkatun manyan ma'aikatun za su iya tabarbarewa.

Maimakon hakan da ya mayar da hankali ga almundahana da wasu boyayyun tsare-tsaren da masana suke korafin cewa su ne suka sanya ma'aikatun cikin matsala tun farko.

4 A rage bashin cikin gida: Duk da kokarin da Buhari ke yi na rage kashe-kashen kudi da ake yi a kasar, jihohin 36 da ake da su duk suna cikin basussuka.

A tsarin tarayya irin ta Najeriya, cin gashin kan su wurin rarraba kudade da jihohi ke yi na shafar al'ummarsu, fiye da rarraba kudi da gwamnatin tarayya ke yi.

Tun da Buhari ya hau mulki ya tallafawa jihohi 27 da ke fama da rashin kudi, da dala biliyan biyu da miliyan dubu dari daya .

Wani rahoto da Bankin bunkasa Afrika ya fitar, ya ce ya kamata a duba irin basussukan da jihohin ke karba.

5 A samu tsayyayun dokoki: Al'ummar Najeriya za su yi kewar kwar jinin Buhari ,da dadewa bayan ya bar mulki (kamar yadda jaridar New York Times ta kwatanta a wani sharhin labarai, wanda aka yi wa lakabi da "A new sheriff in town" watau "Sabon dan sanda ya shigo gari").

Hanya ingantacciya da za a tabbatar, ita ce ya bar abin da za'a dade ana yaba mai

Tun da ba a samun 'yan siyasa kamar Buhari dayawa, toh sai ya tabbatar duk wani tsari da ya kirkiro ya samu kafuwa ta musamman.

Abin da ya kamata a fara da shi shi ne soke kudaden da aka tanada domin tsaro watau 'security votes', da ba a san abin da ake da su ba.

Akwai jan aiki dai a gaban shugaba Buhari.