DSS ta gayyaci Boni Haruna

Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption An gayyaci Boni Haruna ne bayan ya tsaya a matsayin shaida ga Kanar Sambo Dasuki.

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Adamawa kuma tsohon ministan matasa, Mista Boni Haruna domin amsa tambayoyi.

Hukumar ta gayyace shi ne jim kadan bayan ya sanya hannu a matsayin wanda zai tsaya a bai wa tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro, Kanar Sambo Dasuki fasfo dinsa saboda ya je a duba lafiyarsa a kasar waje.

Tuni wasu magoya bayan Boni Haruna suka yi korafin cewa wannan wata bita-da-kulli ce, ganin cewa hukumar ba ta gayyace shi ba sai da ya amince zai tsaya wa Kanar Dasuki.

Har yanzu dai hukumar ta DSS ba ta ce komai dangane da gayyatar da ta yi wa Mista Boni Haruna ba.

Dasuki zai je kasashen waje

Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ta ba da umarnin a gaggauta bai wa Kanar Sambo Dasuki fasfo dinsa, domin ya samu damar zuwa kasar waje domin a duba lafiyarsa.

Sambo Dasuki dai na fuskantar tuhuma ne kan zargin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba da kuma halatta kudaden haram.

Likitan da ke duba shi a Biritaniya ne ya aiko da wasika cewa lallai ya kamata wanda ake tuhuma din ya je can domin a duba lafiyarsa.

Kotun ta bukaci Sambo Dasuki ya gabatar da wani mutum da zai tsaya masa, kuma idan har wa'adin da kotu ta dibar masa na makonni uku ya cika ba tare da ya dawo ba, to kotun za ta kama wannan mutumi a madadin Dasuki.

Sharadi na biyu kuma shi ne ana so ya dawo da fasfo dinsa ga hukumar tsaro ta farin kaya cikin kwanaki biyu da dawowarsa.

Za a ci gaba da zaman kotu da sauraran wannan kara ta Sambo Dasuki a ranar 26 ga watan Nuwamba mai zuwa.