Kotu ta samu likita 'yar Nigeria da laifin kisa ba da niyya ba

Image caption Dr Hadiza Bawa Garba da sauran ma'aikatan jinya

Kotu a Ingila ta samu wata likita da laifin kashe yaro dan shekaru shida bada niyya ba, ta hanyar "sakaci" a asibiti.

Jack Adcock wanda ke fama da ciwon maloho da kuma matsalar zuciya, ya rasu ne a wani asibiti da ke Leicester a watan Fabarairun 2011.

Kotu ta samu Dr Hadiza Bawa-Garba wacce iyayenta 'yan Nigeria ne da laifin kisa ba da niyya ba saboda sakaci, amma kuma an wanke ma'aikaciyar jinya Theresa Taylor, a cikin shari'ar.

A ranar Litinin wata kotun ta samu Isabel Amaro da laifi iri daya da na Dr Hadiza a kan batun mutuwar yaron.

Hadiza Bawa Garba ta yi kuskure a kokarin ceto ran yaron inda ta zaci cewar baya bukatar taimakon yin nunfashi, abin da ya sa ta koma kan wani yaron wanda shi ma yake kwance a asibitin.

A lokacin da Dr Hadiza Bawa Garba ta farga a kan cewar ta yi kuskure, bakin alkalami ya riga ya bushe don kuwa, da ta koma kan dan yaron domin ta taimaka ma shi ya yi nunfashi, rai yayi halinsa.

Dr Hadiza Bawa-Garba 'yar asalin Nigeria ce, iyayenta ne suka turo ta Ingila karatu kuma ta samu shaidar zama likita a makarantar koyan aikin likita ta Leicester Warwick.