NNPC zai biya dillalan mai dala biliyan 413

Image caption An soma fuskantar karancin mai a wasu sassan Nigeria

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC ya ce gwamnatin tarayya ta amince da biyan kudin tallafin mai naira biliyan dari hudu da goma sha uku ga dillalan man fetur.

NNPC ya ce a cikin wata sanarwa, gwamnati ta dauki wannan mataki ne, a wani bangare na kokarin tabbatar da cewa, an kawar da duk wata alama ta karancin man fetur a kasar.

Cikin 'yan kwanakin nan dai ana fuskantar karancin mai a wasu sassan Najeriya.

Kamfanin ya ce, tuni a saki man fetur mai yawa a sassan da suke fuskantar karanci.

Sanarwar ta kuma ce, tuni aka umarci kamfanin PPMC mai alhakin raba mai ga kasar ya tabbatar da cewa, ana kiyaye ka'idojin da ake da su na tabbatar da cewa, man fetur ya isa ga gidajen mai.

Najeriya dai tana da arzikin mai amma lokaci zuwa lokaci kasar kan fuskanci karancin man fetur.