Syria: Bunkasar mulkin iyalan gidan Assad

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bashar al-Assad da Mahaifinsa Hafez Assad

Rikicin Syria ya ja hankalin manyan kasashen duniya, inda wasu ke goyon bayan shugaba Bashar al-Assad, wasu kuma na nuna adawar su da shi.

Iyalan Assad sun yi mulkin Syria fiye da tsawon shekaru arba'in, sai dai kuma ya aka yi suke ci gaba da rike mulkin?

Hafez al-Assad shi ne ya jagoranci gina Syria ta wannan zamanin. Bayan juyin mulkin da aka yi ta yi a Syria, Hafez ya yi amfani da mutanen da yake kewaye da su a matsayinsa na kwamandan rundunar sojin sama kuma ministan tsaro ya yi juyin mulki a shekarar 1970.

Domin ya cigaba da rike mukamin sa, Hafez ya kirkiri tsarin mulkin raba kan jama'a, inda ya nuna cewa shi kadai ne shugaban da zai iya jagorantar kasar.

Hakan ya sa, a lokacin magajinsa ka iya gadar raunanniyar gwamnati. Babban dansa Bassel ne ya kamata ya gaje shi akan mulki, to amma hadarin da yayi a mota da yayi sanadiyyar mutuwarsa a shekarar 1994 ya sa aka bawa kaninsa Bashar.

A lokacin da Bashar ya dare karagar mulki a shekarar 2000 bayan rasuwar mahaifinsu Hafez, mutane da dama sun yi tsammanin cewa za a samu sauyin tsarin mulki, amma kuma abin ba haka ya kasance ba.

Bayan darewarsa karagar mulki, da farko ya cigaba da tafiya da mutanen da mahaifinsa ya yi aiki tare da su, amma daga bisani sai ya sallame su inda ya kawo nasa wadanda yake son tafiya tare da su a matsayin masu bashi shawara.

A mafi yawancin manyan ma'aikatu da kuma hukumomin gwamnati abokan Shugaba Hafez ne ke jagorantarsu tun daga shekarar 1970.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bashal al-Assad da Iyayensa da kuma 'yan uwansa

Bayan ya kawar da mutanen da suka yi aiki da mahaifinsa, Bashar ya kafa nasa tsarin mulkin irin na 'yan birni sannan ya tatile wasu ma'aikatun gwamnati.

A lokacin mulkin Hafez ya yi tafiya ne da dattawa wadanda suka fito daga kauyuka. Shi kuwa Bashar aiki yake da 'yan zamani matasa kuma.

Batun ikon Bashar ya zamo wani zazzafan abin muhawara tun lokacin da aka fara yi masa bore a shekarar 2011.

Akwai alamar tambaya akan cewa wata kila ko iyalansa ne da suka hadar da 'yar uwarsa Bushra da Mijinta marigayi Asef Shawkat da kuma dan uwansa Maher ne ke ingiza shi yana irin wannan mulkin.

Da yawa dai an yi tsammanin cewa zai kasance shugaba ne wanda zai kawo sauyi da yake kuma da niyyar kawo cigaba a Syria, sai dai kuma aka ga akasin hakan saboda ya bi sahun mahaifinsa.