Firai Ministan Romania ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Ponta ya ce yana fata saukarsa za ta sanyaya zuciyar masu zanga-zangar.

Firai Ministan Romania, Victor Ponta, ya yi murabus bayan gagarumar zanga-zangar da aka yi sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan rawa ranar Juma'a, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 30.

A wata sanarwa da ya fitar, Mr Ponta ya ce yana fatan saukarsa daga mulki za ta sanyaya zuciyar masu zanga-zangar.

A ranar Talata ne mutane kimanin 20,000 da suka yi zanga-zanga a birnin Bucharest, inda suka bukaci Mr Ponta da ministan harkokin cikin gida na kasar su yi murabus.

Wani wakilin BBC a kasar ya ce masu zanga-zangar sun fusata ne sakamakon zargin karbar hanci da rashawa da suka yi kamari a kasar, lamarin da ya sa ba a dauki matakan kula da lafiya a gidan rawar ba.