Saraki ya nada shugabannin kwamitoci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Abokan' Saraki sun samu 'manyan' kwamitoci

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya sanar da nadin shugabannin kwamitoci 65 da za su gudanar da ayyukan majalisar.

Abin mamaki, Sanata Saraki ya nada wasu daga cikin wadanda ake kallo tamkar abokan hammayarsa ne a matsayin shugabannin wasu 'manyan' kwamitoci.

Sanata Ahmed Lawan, wanda ya yi takarar kujerar shugaban majalisar tare da Saraki, shi aka bai wa shugaban kwamitin tsaro, a yayin da aka bai wa George Akume shugabancin kwamitin ayyukan soja.

Sanata Danjuma Goje aka bai wa kwamitin kasafin kudi, a yayin da Sanata Rabiu Kwankwaso ya samu kwamitin da ke kula da tsare-tsaren kasa da kuma harkokin tattalin arziki.

Galibin sanatocin da ake kallo a matsayin na hannun damar Sanata Saraki ne, an nada su shugabannin kwamitocin da ake kallo a matsayin 'masu tsoka'.