Abin da ya sa muka gayyaci Dasuki — DSS

Hukumar DSS a Nigeria ta zargi tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki da kin amsa gayyatar da gwamnati ta yi masa.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta, Tony Opuiyo, ta musanta rahotannin da ke cewa jami'anta sun kai samame gidan Kanar Sambo Dasuki ne duk da wata kotun Abuja ta ce a ba shi fasfo dinsa domin ya fita waje yin jinya.

Hukumar ta ce jami'anta sun kai samame gidan Kanar Sambo Dasuki ne saboda ya ki amsa gayyatar da wani kwamitin bincike kan sayen makamai da gwamnati ta kafa ya yi masa, domin ya yi bayanin abin da ya sani game da wasu kudade $2bn da aka kashe wajen sayo makamai a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Hukumar ta ce ba ta da zabi illa ta bi hanyar da doka ta tanada domin ganin ya bayyana a gaban kwamitin.

Sai dai Kanar Sambo Dasuki ya musanta cewa ya taba samun wata wasikar gayyata da ke neman ya bayyana a gaban kwamitin.