Bidiyon Facebook na kara jan hankalin ma'abota shafin

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kamfanin Facebook ya ce a yanzu ana kallon bidiyo fiye da biliyan takwas a shafinsa kowacce rana

Wannan wani gagarumin kari aka samu-- wanda ya nunka abinda ake da shi a watan Afrilu

Matakin da Facebook ya dauka na sanya bidiyo cikin tsarinsa tabbas zai farantawa kamfanoni masu tallace tallace wadanda suka tallata kayayyakinsu

Amma ba kowa ne zai gamsu cewa Facebook zai haura abokin hamayyarsa na You Tube ba

Ta yaya bidiyon cikin Facebook ya samu wannan ci gaba cikin sauri?

Tsarin da facebook ya bullo da shi na yadda bidiyonsa ke aiki a wayoyin salula da kuma shawarartar masu kallo na su kalli karin bidiyo bidiyo ya taimaka wajen samun karuwar masu kallon bidiyon da yake sanyawa

Amma an soki Facebook da rajistar wani bidiyo a matsayin wanda aka kalla idan bidiyon ya na nunawa na dakikoki uku kachal