Wasu daliban Gombe na tsaka mai wuya

Hakkin mallakar hoto gombe government
Image caption Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Daliban Makarantar koyon aikin lauya ta Nijeriya 'yan asalin jihar Gombe sun koka da abin da suka kira mawuyacin hali da suke ciki, sanadiyar rashin ba su kudin tallafin karatu da gwamnatin jihar ta saba bayarwa.

Daliban sun ce wasun su sun ci bashin kudi fiye da naira dubu dari uku kowannensu, domin su biya kudin makarantar da kuma wasu hidindimun karatun, amma har kawo yanzu gwamnatin ba ta waiwaye su ba.

Daliban sun bukaci gwamnatin ta kawo musu dauki.

A duk shekara dai, gwamnatoci da dama kan bai wa daliban jihohinsu tallafin karatu a makarantar aikin lauya saboda tsadar da karatu a makarantar ke da shi.

Jami'an gwamnatin dai sun ce za su gudanar da bincike a kan zargin da daliban suke yi.