Nijar ta kai hari ta sama kan 'yan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin jamhuriyar Nijar

Rahotanni sun ce a karon farko, sojojin Jamhuriyar Nijar sun kaddamar da hare-hare ta sama a kan wasu da take zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

An dai kai harin ne a kusa da wani kauye mai suna Dagaya a lardin Diffa da ke kudancin kasar inda aka yi wa dakarun Nijar din kwanton-bauna.

Gwamnan lardin Diffa Janar Abdou ya tabbatar da kai hare-haren ta sama, sai dai bai yi wani cikakken bayani a kai ba.

Nijar dai ta bi sahun sauran kasashen yankin tafkin Chadi da su ka hadar da Najeriya da Chadi da Kuma Kamaru wadanda su ma su ke kai hare-hare ta sama kan 'yan Boko Haram din.