'Ƙaruwar zubar da ciki a Nigeria'

Hakkin mallakar hoto google maps

Wani sabon bincike da aka yi a Najeriya ya nuna cewa an samu karuwar zubar da ciki a kasar daga shekarar 1996.

Binciken ya nuna cewa adadin masu zubar da ciki sun kai dubu sittin da daya a shekarar 1996, yayin da a shekarar 2012 kuma adadin ya haura mata miliyan daya da dubu dari biyu.

Binciken ya bayyana cewa ba wai saboda karuwar yawan 'yan kasar da aka samu ba ne ake samun karuwar masu zubar da cikin ba, karuwa aka samu a yawan masu zubar da cikin.

Binciken wanda cibiyar Guttmacher da kuma jami'ar Ibadan su ka gudanar, ya nuna cewa duk da yake akwai doka a kan haramta zubar da ciki a Najeriya idan baya zama dole ba, an kiyasata cewa an samu mata masu zubar da ciki 33 a cikin mata dubu guda wadanda shekarunsu ke tsakanin 15 zuwa 49 a shekarar 2012.

Kwararru a bangaren lafiya sun ce mafi yawancin zubar da cikin a boye ake yin sa, kuma akwai hadari a tattare da hakan, saboda ba kwararru ne ke yi ba.

Wani bincike kuma da kungiyar likitoci ta kasar ta gudanar ya nuna cewa yammata fiye dubu hamsin na mutuwa a duk shekara saboda hadarin da su ke shiga a yayin zubar musu da ciki.