Manhajoji na yi wa masu salula leken asisri

Image caption Manhajojin salula masu yi wa mutane leken asiri

Manhajoji da yawa na wayoyin Apple da Android su na yi ma masu amfani da wayoyin leken asiri, inda suke aikawa da bayanan mutane zuwa ga wasu.

Wasu masu bincike daga cibiyar ilimin fasaha ta Massachusetts, da jami'o'in Harvard da Carnegie-Mellon sun gudanar da bincike a kan wasu manhajoji 110 da suke rumbunan manhaja na Google Play da kuma Apple.

Masu binciken sun gano cewa kashi 73% na manhajojin Android suna amfani da hanyoyin aikawa da sakonnin Emai na mutane, sannan kashi 47% na manhajojin Apple suna amfani da bayanan daga inda masu wayoyin suke amfani da su.

Wata kungiyar dake fafutikar kare sirrin mutane ta kasa da kasa, Privacy International, ta ce wannan ya nuna irin butulcin da wayoyin salula ke yi wa masu amfani da su.

Binciken mai take "Wanene yasan wani abu a game da ni" ya yi nazari a kan fitattun manhajojin Abdroid 55, da kuma wasu 55 na Apple.