An soma bukukuwan kawo karshen Ebola a Saliyo

Hakkin mallakar hoto AP

Kasar Saliyo ta soma bukukuwa gabanin ranar Asabar da ake shirin ayyana kasar a matsayin kasar da babu cutar ebola a cikinta.

Amma kungiyar Likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta ce kimanin kashi tamanin cikin dari na mutanen da suka warke daga cutar na fama da wasu matsaloli kamar ciwon gabobi da kuma rashin karfin jiki.

Sauran mutanen da suka warke sun ce sun daina gani, sai dai masu bincike na kokarin gano dalilin hakan.

Kungiyoyin mutanen da suka warke daga cutar sun ce babbar matsalar da suke fuskanta ita ce ta kyamar da ake nuna musu, da kuma jin damuwar cewa sun warke yayin da wasu suka mutu.