SSS: Sambo Dasuki na tsaka mai wuya

Image caption Dasuki ya ce zai je kasar waje jinya saboda ciwon daji

Rahotanni daga Nigeria na cewa, jami'an tsaro na farin kaya SSS sun kai samame gidan tsohon mai bai wa shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki a Abuja babban birnin kasar.

Bayanai sun nuna cewa jami'an hukumar sun bukaci Dasukin da ya amsa wata gayyata zuwa ofishinsu domin amsa tambayoyi amma kanar din ya ce ba zai amsa gayyatar ba tun da ba sammace ba ne na kamu.

Hukumomin kasar sun shigar da karar Kanar Sambo Dasuki a gaban kuliya, inda suke zarginsa da mallakar makamai ba bisa kaida ba, da kuma safarar kudaden haram.

Majiyoyi da ke kusa da tsohon mai bawa shugaban kasa shawara sun shaida wa BBC cewa, da safiyar ranar Alhamis ne jami'an hukumar ta SSS suka ziyarci gidansa.

Sai dai majiyoyin sun ce Kanar Dasuki ya ce idan gayyata ce, to yana da hurumin ya ki amsa gayyatar su, amma idan kama shi suke so su yi, ba zai hana su kama shi ba idan har suna da sammace.

Bayanai sun nuna cewa tun a ranar Laraba, Kanar Sambo Dasuki ya yi niyyar tafiya waje don duba lafiyar sa, bayan wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukuncin a bashi fasfo.

Sai dai wasu na kusa da Kanal Sambo Dasukin sun shawarce shi da ya dakatar da tafiyar, domin kamar yadda suka ce, sun samu labarin an shirya kama shi idan ya je filin saukar jiragen sama.

Hakan ta sa Kanar Dasuki ya fasa tafiyar.