'Yan tawayen Syria sun samu 'yar nasara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kan 'yan tawayen Syria a rabe yake

Rahotanni daga Syria na cewa 'yan tawaye sun kwace iko da wani gari wanda ke da mahimmanci daga birnin Damascus zuwa Aleppo.

Masu rajin kare hakkin 'yan Syria, sun ce sun kwace iko da garin Morek wanda ke arewacin birnin Hama a kan hanyar zuwa birnin Aleppo.

Kungiyar Nusra Front mai alaka da kungiyar Alka'ida ta taya kungiyar jihadi ta Jund al Aqsa murnar jagorantar wannan nasarar.

Sun yi shagulgula a tare saboda wannan nasarar, a wani mataki da ake kallo alama ce ta sulhu a tsakaninsu.

A ranar Laraba, dakarun gwamnati suka ce sun kwace iko da wata hanyar wacce ita ma za ta kai mutum zuwa birnin Aleppo.