An rantsar da sabon shubagan Tanzania

An rantsar da sabon shugaban Tanzania, John Magufuli a wani biki a birnin Dar es Salam.

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, yana daga cikin shugabannin kasashen da suka halarci bikin rantsarwar.

Duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a birnin Dare es Salam, jama'a sun yi tururuwa domin shaida rantsar da sabon shugaban kasar John Magufuli.

Shi dai sabon shugaban, wanda ake yi lakabi da "Bulldozer" ya yi jawabi na neman sasantawa, yana mai cewa, masu adawa da shi za su karfafa shi domin ya sauke nauyin da jama'a suka dora masa.

Mr Magufuli ya yi kira ga masu adawa da shi su zo su yi aiki tare.