Boko Haram: An rufe makarantu 150 a Diffa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Boko Haram ta lalata wurare sosai a Diffa

An rufe makarantu 150 a yankin Diffa na jamhuriyar Nijar saboda hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.

Ofishin da ke kula harkokin jin kai na majalisar dinkin duniya wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, ya ce rufe makarantun ya janyo yara 12,631 ba sa zuwa makaranta.

Hukumar ta ce lamarin kuma ya janyo malamai sun kaurace wa makarantun a yayin da mutane kuma ke ci gaba da ficewa daga yankin.

Sanarwar ta ce "Daliban a yanzu suna sansanonin 'yan gudun hijira kuma babu makarantu a can."

An rufe makarantu da dama a Najeriya da Nijar sakamakon hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram abin da ya jefa makomar dubban yara cikin rashin tabbas.

A yanzu haka dai gwamnatin Nijar na aiki tare da majalisar dinkin duniya domin fitar da wani tsari ta yadda yaran za su koma yin karantu a wasu yankunan da babu hadari.