Biritaniya za ta kwashe 'yan kasarta daga Masar

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption David Cameron ya yi imanin cewa bom aka saka cikin jirgin da ya fadi a Masar

A ranar Juma'a ne Biritaniya za ta fara kwashe dubban 'yan kasarta da suka makale a Masar.

Wannan mataki na faruwa ne bayan gwamnatin kasar ta dakatar da jiragenta tashi zuwa birnin Sharm-el-Sheikh da ake zuwa yawon bude ido a Masar, bayan jirgin saman Rasha ya fadi jim kadan da tashinsa daga birnin.

BBC ta fahimci cewa masu bincike a Biritaniya sun gamsu cewa an sanya bom a wani wuri a cikin jirgin kafin ya tashi.

Shugaba Obama ya ce Amurka ta dauki batun amfani da bom a cikin jirgin da muhimmanci sosai.