An dakatar da gina bututu daga Canada zuwa Amurka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wurin aikin gina bututun man

Shugaba Obama na Amurka ya yi watsi da batun shirin gina bututun mai cike da cece-kuce daga kasar Canada zuwa Amurka.

Shugaban ya ce bututun mai na Keystone XL ba zai yi wa Amurka amfanin komai ba, kuma ba zai bunkasa tattalin arziki ba, ko kuma bunkasa samar da wutar lantarkin kasar.

Mr Obama ya kuma kara da cewar amincewa da wannan shawarar na nufin rage darajar shugabancin Amurka a lokacin da ake so a dauki mataki domin rage sauyin yanayi.

Masanantar man tana ta kamun kafa a kan gina bututun man, kuma masu adawa da suke takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar Republican sun soki shawarar da Mr Obama ya yanke, inda Jeb Bush ya kira da cewar tamkar hari ne a kan tattalin arzikin Amurka.