Jaridar Charlie Hebdo na shan suka a Rasha

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Charlie Hebdo na janyo cece-kuce

Jaridar nan mai barkwanci ta kasar Faransa, Charlie Hebdo, na fuskantar suka daga al'ummar Rasha a kan zanen barkwancin da ta yi a kan hadarin jirgin da ya fadi a Masar.

Zanen ya nuna wani dan bindigar kishin Islama da gemu na daukar matakan kariya yayin da sassan jirgin da gawarwaki ke fadowa daga sama.

An kuma yi wani rubutu da ke cewa Daesh-- watau kungiyar IS na kenan, tana cewa Rasha ta kara zafafa hare-harenta".

Wasu jami'ai da 'yan siyasa sun yi Allah-wadai da zanen yayin da masu amfani da hanyar sadarwa ta twitter kuma su ka yi watsi da shi a matsayin wani abin takaici.

A farkon wannan shekarar , Jaridar Charlie Hebdo ta samu goyan bayan kasashe da dama bayan da masu tsaurin kishin Islama su ka kashe mutane 12 a ofishinta da ke Paris.