Putin ya hana tashin jiragen sama zuwa Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kwararru sun soma bincike kan tarkacen jirgin

Shugaba Putin ya ba da umurnin dakatar da zirga-zirgar duka jiragen sama daga kasar Rasha zuwa Masar, har sai an gano abin da ya janyo faduwar jirgin saman kasarsa a yankin Sinai.

Fadar gwamnatin Rasha, ta ce kasar za ta yi aiki tare da gwamnatin Masar domin inganta tsaro a harkokin jiragen sama na kasar, kafin jirage su koma zirga-zirga tsakanin kasashen biyu.

Sai dai a cewar Rasha, hakan ba yana nufin bane sun amince a kan cewar 'yan ta'adda ne suka janyo hadarin jirgin wanda ya hallaka mutane 224.

Kwararru daga Rasha na gudanar da nazari a kan tarkacen jirgin saman ko za su gano abubuwan fashewa.

Biritaniya da Amurka sun ce bisa dukkan alamu da bam ne ya janyo faduwar jirgin saman.