Mutane dubu 157 ne kutsen Talk Talk ya shafa

Image caption Kamfanin sadarwa na Talk Talk

Kamfanin sadarwa na Talk Talk da aka yi wa kuste ya wallafa wani rahoto a shafinsa na intanet inda ya ce kimanin masu mu'amala da dubu 157 ne a ka saci bayanansu.

Fiye da bayanan asusun a jiya na bankunan mutane dubu 15 da dari 6, da kuma wasu karin bayanan bankuna aka satar wa mutane a lokacin kutsen.

Kamfanin na TALK Talk ya shawar ci masu mu'amala da shi da su ci gaba da daukan matakan kariya daga amsa waya ko karbar sakon email daga bata gari.

A cikin wannan makon ne 'yan sanda suka bayar da belin wani yaro dan shekara 16 wanda shi ne na hudu da aka kama bisa laifin yin kutsen.

Tun bayan da labarin kutsen da aka yi wa Talk Talk ya yadu, farashin hannayen jarinsa sun yi kasa.

Kamfanin ya tuntubi masu mu'amala da shi da matsalar kutsen ta shafa, sannan kuma zai kara tuntubar wasu a cikin kwanaki masu zuwa.

Mutane hudun da aka kama bisa zarginsu da kutsen sun hada da dan Ireland ta Arewa, da wani daga London ta yamma, da kuma wani daga Staffordshire sannan kuma dayan daga Norwich.