Mutane na barin gidajensu a Burundi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani wuri da aka fuskanci tashin hankali a Burundi

Mutane da dama suna barin gidajensu daga sassan daban daban na Bujumbura, babban birnin kasar Burundi, gabannin cikar wa'adin da gwamnatin kasar ta debarwa 'yan bindiga akan su ajiye makamansu ko kuma su fuskanci fushinta.

Wa'adin dai ya cika ne da tsakar daren jiya.

Mutane kusan dari biyu ne aka kashe a lokacin rikicin kasar a watan Aprilu, bayan da shugaba Peirre Nkurunziza ya ce zai tsaya takara a karo na uku.

An dai fahimci cewa ba bu wani da ya bayyana domin ya mika makaminsa kamar yadda gwamnatin Burundi ta nemi yan kasar su yi.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma shugabannin kasashen duniya sun yi gargadin cewa Kasar ta Burundi na gab da fadawa cikin mumunnan yanayi.