'Ana ci gaba da kashe jama'a a Burundi'

Hakkin mallakar hoto

Ci gaba da kazancewar rikicin siyasa a Burundi, ya sa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kiran a kawo karshen kar-kashe jama'a da ake yi a kasar.

A cikin wata sanarwa, Mista Ban Ki-moon ya ce yanzu, ganin gawarwakin mutanen da ake kashewa ba tare da shari'a ba a babban birnin kasar Bujumbura, abu ne da ya zama ruwan dare.

Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundin ya bai wa 'yan bindiga a kasar wa'adin zuwa karshen makon nan da su ajiye makamansu.

Faransa ta yi kiran a gudanar da wani taron gaggawa na kwamitin tsaro na MDD domin tattauna rikicin siyasar Burundin, wanda aka fara a watan Afrilu bayan shugaba Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta zarcewa a shugabancin kasar karo na uku.