Ana zabe a Myanmar

Hakkin mallakar hoto BBC Chinese
Image caption Masu zabe a Mynamar

Yau ne ake babban zabe a Myanmar wanda kuma ake kyautata zaton zai kawo karshen gwamnatin da soji ke marawa baya da ta kwashe kimanin shekaru hamsin tana mulkar kasar.

Sama da 'yan kasar miliyan 30 ne ake saran za su kada kuri'a.

Tuni aka fara ganin dogayen layuka a mazabu daban daban a fadin kasar, tun gabanin bude rumfunan zaben.

Alamu na nuna jam'iyyar da Aung San Suu Kyi ke jagoranta ta National League for Democracy za ta iya lashe mafi yawancin kujerun majalisar dokiki a zaben na ranar Lahadi.

Sai dai kuma jam'iyar tana bukatar ta samu kaso biyu bisa uku na kujerun majalisar, kafin ta samu rinjayen da za ta kafa gwamnati.

Wasu kungiyoyin kare 'yancin bil'adama na kasa da kasa sun ce akwai matsaloli tare da shirin zaben saboda tauye wa dubban musulmai hakkinsu na kada kuri'a da kasar ta yi.