PNDS ta ba wa Issoufou takara

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Niger, Muhamadou Issoufou ya karbi tutar jam'iyyar PNDS.

Jam'iyar PNDS Tarayya mai mulki a jamhuriyar Nijar ta kaddamar da shugaban kasar mai barin gado, Mahamadou Issoufou a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasar da za a yi a farkon shekarar 2016.

Jam'iyar ta dau wannan matakin ne yayin wani babban biki da ta shirya, a babban birnin kasar Yamai, ranar Asabar.

Bikin dai ya samu halartar dubban magoya baya da kuma shugabannin jam'iyun siyasa da abokan arziki na ciki da wajen kasar.

Magoya bayan jam'iyar sun ce sun jaddada masa goyon bayansu ne saboda ci gaban da ya jawo wa kasar daga hawansa kan karagar mulki kawo yanzu.

Saboda haka ne suka ce suna son ayyukan alhairin da ya fara su dore.

Sai dai 'yan adawa na ganin da sake inda suke ganin cewa Nijar ba ta taba fuskantar koma baya ba kamar a lokacin mulkin na Mahamadou Isoufou.