Shagulgulan karshen cutar ebola a Saliyo

Al'umomin kasar Saliyo suna gudanar da shagulgula, a yayin da suke dakon Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana kasar a matsayin wadda ta kawar da cutar Ebola baki daya.

Barkewar cutar a kasar ta yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane dubu 4 a cikin watanni 18 da suka gabata.

Dubban mutane ne dai suka fito a daren jiya domin nuna farin ciki da kwashe kwana 42 a kasar ba tare da an samu ko da mutun guda da ya kamu da cutar ba.

Da yawa daga cikin mutanen sun tattaru ne a kusa da wata babbar bishiyar auduga a tsakiyar birnin Freetown, inda wasu suke kunna kendiri domin tunawa da wadanda cutar ta kashe, wasu kuwa ke ta tika rawar murna abin su.