WHO: Babu sauran Ebola a Saliyo

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumar lafiya ta duniya ta baiyana cewa an kakkabe cutar Ebola daga Saliyo bayan shafe tsawon kwanaki 42 ba tare da samun kwayar cutar ba.

Mutane kusan 4000 ne suka rasu a sakamakon cutar a kasar Saliyo a watanni goma sha takwas da suka wuce.

A daren jiya jama'a sun yi ta shagulgulan murna a titunan Freetown babban birnin kasar domin murnar cigaban da aka samu na kawo karshen cutar da kuma tunawa da wadanda cutar ta hallaka.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a yanzu kasar ta Saliyo za ta shiga wani sabon babi na kwanaki 90 domin kara sa ido sosai ko za a sami wasu sabbin kamu.

Tuni dai aka kawar da cutar daga Liberia amma an cigaba da samun bullar ta a kasar Guinea.