Wasu 'yan majalisa na shirin tsige Dogara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Yakubu Dogara

Wasu 'yan Majalisar wakilan Najeriya sun yi barazanar tsige shugaban majalisar, Yakubu Dogara sakamakon nuna son kai wajen rabon kwamitoci.

Tun dai bayan da shugaban majalisar wakilan ya raba shugabancin kwamitoci a zauren wasu 'yan majalisar suke nuna rashin jin dadinsu da yadda aka raba kwamitocin.

'Yan majalisar wakilai daga jam'iyyar APC mai rinjaye su ne suka fi nuna adawa da yadda aka raba shugabancin kwamitocin.

Sun yi zargin cewa an bai wa 'yan jam'iyyar PDP akasarin kwamitocin masu "romo".

Garba Chede, dan majalisar wakilai na tarayya daga jihar Taraba, ya shaida BBC cewa za su dauki matakai da ka iya kai wa ga a tsige shugaban nasu matukar bai sake fasalin rabon kwamitocin ba.

Sai dai kuma bangaren shugaban majalisar sun ce wannan zance ne marar tushe.

A ranar Litinin ne ake sa ran shugaban majalisar wakilan zai kaddamar da shugabannin kwamitocin majalisar da mataimakansu.