'Intanet zai zama 'yanci a Birtaniya'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firaiministan Birtaniya, David Cameron

Firaiministan Birtaniya, David Cameron ya sha alwashin cewa dukkan gidaje da wuraren sana'a za su samu damar yin amfani da intanet mai sauri a shekarar 2020.

Ya ce "tsarin intanet a karni na 21 'yancin dan adam ne ba wai wani kayan gabas ba ne ko kuma wani abin yin gayu".

Mista Cameron yana son bullo da wani yanayi da zai mayar da samun damar amfani da intanet a matsayin bangaren 'yancin dan adam.

Hakan zai sanya damar amfani da intanet din a matsayin 'yancin dan adam kamar samar da ruwan sha da wutar lantarki.

A 2010, gwamnatin ta Birtaniya ta yi wa 'yan kasar alkawarin sama musu intanet wanda ya fi na kowacce kasa a tarayyar turai karfi da sauri a shekarar 2015.

Shi ma sakataren al'adun kasar ta Birtaniya, Jeremy Hunt, a shekarar 2012 ya yi irin wannan alkawari na samar da tsarin intanet da ya fi kowanne a nahiyar turai karfi da sauri, a 2015.

Ya kuma bayyana tsarin intanet mafi sauri da wanda zai ba wa mutum damar shiga yanar gizo ya kuma sauke wata manhaja ko kuma wani bayani mai nauyin megabites 24 cikin dakika daya kacal.

Sai dai kuma hukumar kula da sadarwa ta Ofcom ta bayyana intanet mafi sauri da sauke bayani mai nauyin megabites 30 a cikin dakika daya kacal.

Yanzu haka dai kaso 83 da al'ummar Birtaniya suna da tsarin intanet mai karfin sauke bayani mai nauyin megabites 24 a cikin dakika daya kacal.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Za a samar da tsarin intanet din mai karfi da sauri ta hanyar runbun broadband

Ana kuma saran nan da 2017 kason zai karu zuwa 95.