Jamus za ta iya da 'yan cirani

'Yan cirani sun yi cirko-cirko a iyakar kasar Jamus Hakkin mallakar hoto AFP getty
Image caption Yawancin 'yan ciranin sun fito ne daga kasashen da ake tashe-tashen hankula irinsu Iraqi da Syria.

Shugaban babban bankin kasar Jamus , ya ce kasar za ta iya da yawan baki 'yan cirani da suke neman mafakar siyasa ba kuma tare da hakan ya sanya sauran kasafin kudin Jamus cikin halin ni 'ya su ba.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Tagesspiegel, Mr Jens Weidmann ya ce za a iya shawo kan matsalar 'yan ciranin idan har Jamus za ta shigar da su cikin harkokin yau da kullum, musamman sama musu ayyukan yi wanda hakan zai kara bunkasa tattalin arzikin kasar.

Fiye da mutane miliyan 1 ake sa ran za su nemi mafakar siyasa a kasar Jamus kafin wannan shekarar ta kare.