Tashin hankali ya barke a Wukari

'Yan sandan Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mazauna garin Wukari sun ce tun a daren jiya ake ta jin karar harbe-harbe.

Rahotanni daga garin Wukari na cewa tashin hankali ya barke a daren jiya a cikin garin, bayan kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Taraba ta soke zaben gwamnan jihar tare da bada umarnin a rantsar da Hajiya Aishatu Jummai Alhassan ta jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar.

Mazauna garin sun shaidawa BBC cewa tun da misalin karfe 12 na daren jiya su ke ta jin karar harbe-harbe ta ko ina, kafin asuba har an kashe musu mutane akalla 16 da raunata fiye da 20.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Taraba, DSP Joseph Kwaji ya tabbatar da aukuwar tashin hankalin, amma yace jami'ansu na kokarin tabbatar da zaman lafiya a garin na Wukari.