An kama dan Boko Haram a filin jirgi

Image caption An dai kama wanda ake zargin ne a filin jirgin sama

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama daya daga cikin 'yan kungiyar Boko Haram guda 100 da take nema ruwa-a-jallo.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriyar, Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya fitar, rundunar ta ce a ranar Lahadi ne hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman kasar ta kama wani mutum mai suna Chindo Bello wanda kuma ake kyautata zaton dan kungiyar Boko Haram.

An kama mutumin ne a lokacin da yake kokarin hawa jirgin kamfanin Aero Contractors daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja zuwa Lagos.

Tuni kuma hukumar ta mika wa rundunar sojin kasar mutumin domin a ci gaba da yi masa bincike.

A 'yan makonnin da suka gabata ne dai rundunar sojin ta Najeriya ta wallafa sunayen mutane 100 wadanda ta ce tana nema ruwa-a-jallo saboda zargin da ake yi musu da hannu wajen kai hare-hare a wurare daban-daban a fadin kasar.