Taron kasashen Afrika kan zaman lafiya

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Litinin za a bude taro kan zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afrika a Dakar, babban birnin kasar Senegal.

A cikin kwanaki biyu da za a gudanar da taron, shugabannin kasashen Afrika da ministoci da kuma kwararru kan aikin soji za su yi nazari a kan hanyoyin karfafa tsaro da zaman lafiya a nahiyar.

Taron na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu kasashen Afrika ke fuskantar tashe-tashen hankula.

Mutane sama da 500 ake sa ran za su halarci taron, ciki har da kungiyoyin fararen hula da malaman jami'oi.