An rantsar da sabon shugaban INEC

Hakkin mallakar hoto Aso Rock Nigeria
Image caption Farfesa Mahmood Yakubu ya sha alwashin kawo sauye-sauye a hukumar zaben Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon shugaban hukumar zaben kasar, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

A lokacin da yake rantsar da shugaban na INEC, Shugaba Buhari ya ce ba zai tsoma baki a harkokin hukumar ba.

Shugaban na Najeriya ya yi kira ga 'yan kasar da su bayar da gagarumar gudunmawa wajen ganin mulkin dimokradiyya ya dore, ta hanyar tabbatar da zabe na gari.

A nasa bangaren, shugaban hukumar zaben ya sha alwashin gudanar da aikinsa ba tare da nuna son kai ba.

A ranar 22 ga watan Oktoba ne Shugaba Buhari ya nasa Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar zaben, wanda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.

Gabanin nadin nasa dai, kwamishiniyar hukumar, Hajiya Amina Zakari ce take shugabancin hukumar a matsayin rikon-kwarya.