Shugaban MTN ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An ci tarar MTN ne saboda ya ki rufe layukan mutanen da ba su yi rijista ba.

Shugaban kamfanin MTN ya yi murabus sakamakon tarar $5.2bn da hukumar sa ido kan kamfanonin sadarwa a Najeriya ta ci kamfanin.

A wata sanarwa da ya sanyawa hannun, shugaban kamfanin Sifiso Dabengwa ya ce ya yi murabus ne nan-take, yana mai cewa ya dauki matakin ne "domin kare martabar kamfanin da masu zuba jari a cikinsa".

Mr Dabengwa ya zama shugaban kamfanin ne a shekarar 2011.

An nada Phuthuma Nhleko a matsayin shugaban-riko na MTN zuwa watanni shida, a yayin da kamfanin ke neman wanda zai maye gurbin Mr Dabengwa.

An ci kamfanin tara ne saboda ya ki rufe layukan mutanen da suka ki yin rijista har wa'adin yin rijistar ya wuce.

Tarar da aka ci kamfanin ta ninka ribar da ya samu a shekarar da ta wuce.

An bai wa MTN tsawon makonni biyu domin ya biya tarar, wato zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba.

Sai dai kamfanin yana ci gaba da tattauna wa da mahukuntan Najeriya kan yadda za a rage masa tarar.

Reshen MTN na Najeriya shi ne reshe mafi girma, inda yake da wadanda suka mallaki layukansa guda miliyan 28 da dubu 500.