Jam'iyyar Aung San Suu Kyi na gab da samun nasara

Aung San Suu Kyi Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jagorar 'yan adawa a Myanmar

Babbar jam'iyyar adawa ta Myanmar, Jam'iyyar National League, ta ce tana sa ran lashe kashi 70 ciki dari na kujerun 'yan majalisar dokoki a zaben da aka yi ranar Asabar.

Ko da yake kawo yanzu kujeru kalilan ne kawai aka bayyana, shugabar jam'iyyar, Aung San Suu Kyi, ta bayyana alamar samun nasara.

Ta shaidawa wasu dumbin magoya baya da ke shewa, cewar kowa ya tsinkayi sakamakon wannan zabe.

To amma a karkashin tsarin mulkin kasar, an yiwa sojoji tanadin kashi ashirin da biyar cikin dari na kujeru a majalisar dokokin kasar, don haka jam'iyyar adawa na bukatar samun kashi biyu cikin dari na kuru'un da suka rage gabanin ta kafa gwamnati.