'Ana samun nasarar a riga-kafin Sankarau'

Hakkin mallakar hoto spl
Image caption Masana kiwon lafiya na son a ci gaba da gano bakin zare kan kawar da cutar

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce shirin riga-kafin sankarau a Afrika ya samu gagarumar nasara.

An yi wa sama da mutane miliyan dari biyu riga-kafin a kasashe goma sha shida a wani abu da aka sami na kasashen da suka fi samun cutar sankarau din a nahiyar kama daga Gambiya zuwa Habasha.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce mutane hudu ne kawai suka kamu da cutar sankarau a shekara ta 2013 duk fadin yankin, wanda a baya ya fuskanci mutuwar dubban mutane a kowace shekara.

A shekara ta 2010 ne aka fara aikin riga-kafin.