Buhari ya yi wa 'yan Nigeria ba-zata

Image caption Kachukwu bayan ya sha rantsuwa

'Yan Najeriya na bayyana ra'ayoyi daban-daban kan ma'aikatu da Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa ministocin da ya nada.

'Yan kasar da dama sun yi mamakin ma'aikatun da aka bai wa wasu daga cikin ministocin.

Mutum na farko da ya ba da mamaki ita ce Mrs Kemi Adeosun, wacce aka bai wa mukamin ministar kudi.

Misis Kemi tana cikin ministocin da ke da karancin shekaru.

Ko da ya ke ta taba zama kwamishiniyar kudi a jihar Ogun, mutane da dama na ganin ba ta da gogewar da za ta iya tafiyar da ma'aikatar kudin kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a Afirka.

Mr Okechukwu Enelemah, mutumin da aka yi tsammanin za a bai wa mukamin ministan kudi, shi ne ministan masana'antu da kasuwancin da zuba jari.

'Fashola-Sarkin Aiki'

Shi kuwa tsohon gwamnan jihar Lagos, Babatunde Fashola - wanda ya kawo sauye-sauye a cibiyar kasuwancin Najeriya - an ba shi aikin da ya fi na kowanne girma a cikin ministocin.

Shi ne zai jagoranci sabuwar ma'aikatar makamashi da ayyuka da samar da gidaje.

Image caption Ministan harkokin Ma'adinai

Shugaba Buhari ya bai wa 'yan kasar mamaki saboda nadin da ya yi wa tsohon Babban Hafsan Sojin kasar, Janar Abdurrahman Dambazau a matsayin ministan harkokin cikin gida.

An yi tsammanin za a ba shi ministan tsaron kasar.

'Ina Amina Mohammed?'

Sai dai sabanin hakan, Janar Mansur Dan-Ali ne ministan tsaro.

Fitaccen marubuci kuma mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum, Adamu Adamu, wanda ya karanta fannin Akanta, kuma yana da kusanci da Shugaba Buhari, ya zama ministan ilimi.

An yi tsammanin Amina Mohammed - tsohuwar mai bayar da shawara ga Sakatare Janar Majalisar Dinkin Duniya kan muradun ci gaban kasashe - za ta zama ministar tsare-tsaren kasa, amma sai aka ba ta ministar muhalli.