Ministocin Buhari sun samu ma'aikatu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fashola ne ke rike da babbar ma'aikata

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanar da ma'aikatun da ministocin da ya rantsar za su jagoranta.

Shugaban ya bukace su da su zagen-dantse wajen gudanar da ayyukan da aka basu, yana mai cewa 'yan Najeriya sun zuba ido su ga irin rawar da za su taka wajen ci gaban kasar.

Tsohon gwamnan jihar Lagos, Babatunde Raji Fashola shi aka nada ministan makamashi, ayyuka da kuma samar da gidaje a yayin da aka bai wa Kemi Adeosun, ma'aikatar kudi.

Abdurrahman Dambazau shi ne ministan harkokin cikin gida, a yayin da aka bai wa Mansur Dan-Ali ma'aikatar tsaro sai Adamu Adamu da aka nada a matsayin ministan Ilimi.

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi shi ne aka bai wa ma'aikatar sufuri sai kuma Mr Okechukwu Enelemah a matsayin ministan cinikayya da kasuwanci.

Amina Mohammed ita aka bai wa ma'aikatar muhalli a yayin da Muhammed Bello ya zama ministan babban birnin tarayya, Abuja sai kuma Solomon Dalung ministan harkokin wasanni da matasa.

Cikakken jerin sabbin ministoci da ma'aikatunsu;

 1. Chris Ngige - Ministan Kwadago da ingantuwan aiki
 2. Kayode Fayemi- Ministan Harkokin Ma'adinai
 3. Rotimi Amaechi - Ministan Sufuri
 4. Babatunde Fashola - Ministan Makamashi, ayyuka da samar da gidaje
 5. Abdulrahman Dambazau- Ministan harkokin cikin gida
 6. Aisha Alhassan - Ministar harkokin mata
 7. Ogbonaya Onu- Ministan Kimiyya da Fasaha
 8. Kemi Adeosun - Ministar Kudi
 9. Abubakar Malami - Ministan Shari'a
 10. Sen Hadi Sirika - Karamin Ministan a harkokin zurga-zurgar jiragen sama
 11. Barr. Adebayo Shittu - Ministan Sadawar
 12. Suleiman Adamu - Ministan samar da ruwan sha
 13. Solomon Dalong - Ministan Wasanni da harkokin Matasa
 14. Ibe Kachikwu - Karamin Ministan harkokin Man Fetur
 15. Osagie Ehanire - Karamin Ministan Lafiya
 16. Audu Ogbeh - Ministan Ayyukan Gona
 17. Udo Udo Udoma - Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa
 18. Lai Mohammed - Ministan Yada Labarai
 19. Amina Mohammed - Ministar Muhalli
 20. Ibrahim Usman Jibril - Karamin Ministan Muhalli
 21. Hajia Khadija Bukar Ibrahim - Karamar Ministar Harkokin Waje
 22. Cladius Omoleye Daramola - Karamin Ministan Naija Delta
 23. Prof Anthony Onwuka - Karamin Ministan Ilimi
 24. Geoffrey Onyema - Ministan Harkokin Waje
 25. Mansur Dan Ali - Ministan Tsaro
 26. Barr James Ocholi - Karamin Ministan Kwadago
 27. Zainab Ahmed - Karamar Ministar Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren kasa
 28. Okechukwu Enelamah - Ministan Cinikayya da Kasuwanci da kuma Masana'antu
 29. Muhammadu Bello - Ministan Abuja
 30. Mustapha Baba Shehuri - Karamin Ministan Makamashi da Ayyuka
 31. Aisha Abubakar - Karamar Ministar harkokin cinikayya
 32. Heineken Lokpobiri - Karamin Ministan ayyukan gona
 33. Adamu Adamu- Ministan Ilimi
 34. Isaac Adewole- Ministan Lafiya
 35. Abubakar Bawa Bwari - Karamin minista harkokin Ma'adinai
 36. Pastor Usani Uguru - Ministan Naija Delta