Me ku ka sani kan sabon shugaban EFCC?

Hakkin mallakar hoto efcc
Image caption Ibrahim Magu ya yi fice wajen gudanar da tsauraran tambayoyi ga manyan mutanen da ake zargi da karbar hanci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Magu a matsayin sabon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa.

An nada shi ranar Litinin bayan an sauke Ibrahim Lamorde daga kan mukamin, wanda ya hau kan mukamin tun a shekarar 2011.

Mr Magu na cikin mutanen da suka fara aiki da hukumar ta EFCC a lokacin shugabancin Nuhu Ribadu.

Ana kallonsa a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana, wanda ke kymar cin hanci da rashawa.

A wancan lokacin shi ne ke kula da sashen da ke gudanar da bicike kan manyan jami'an gwamnati.

Gwamnoni na tsoronsa

An ambato wasu tsofaffin jami'an gwamnati, cikinsu har da tsofaffin gwamnoni, na cewa Mr Magu ya kware wajen gudanar da tambayoyi da titsiye mutum.

Wata kafar watsa labarai ta ambato wani tsohon gwamna na cewa Mr Magu ya taba yi masa tambayoyi irin na yaya-mahaifiyarka-ta-haife-ka a lokacin da yake gudanar da bincike a kansa.

Wasu majiyoyi na cewa Mr Magu ne ya wuce gaba a binciken da aka yi kan shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, lokacin da yake gwamnan jihar Kwara kan dalilan da suka sa Societe Generale ya rushe.

Kazalika, Mr Magu ya gudanar da bincike kan tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori, wanda aka samu da laifukan halasta kudaden haramun a kasar Biritaniya.

A shekarar 2008 ne aka zargi Mr Magu da laifin boye bayanan wasu manyan 'yan siyasa ba bisa ka'ida ba, sai dai ya musanta zargin.

Amma duk da haka shugabar riko ta EFCC a wancan lokacin, Farida Waziri, ta sa an yi bincike a gidansa.

Daga bisani dai an koma da shi rundunar 'yan sanda, sannan aka dakatar da shi daga aiki ba tare da ba shi albashi ba.

Sai dai bayan Lamorde ya zama shugaban hukumar ya mayar da Mr Magu a kan aiki, inda ya zama daya daga cikin manyan jami'an hukumar, har zuwa ranar Litinin lokacin da aka nada shi kan shugabancin hukumar na riko.